Da dumi-dumi: Gwamna El-Rufai ya rantsar da sabbin kwamishinoni (hotuna)

Da dumi-dumi: Gwamna El-Rufai ya rantsar da sabbin kwamishinoni (hotuna)

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmed El-Rufai ya rantsar da sabbin kwamishinoni 13 a ma’aikatun gwamnatinsa karo na biyu.

Gwamna El-Rufai ya gabatar sunayen mutane 14 da yake so su zama mambobin majalisarsa a gaban majalisan dokoki Jihar, amma sai majalisar ta ki amincewa da sunan wanda ya gabatar a matsayin kwamishinan ma’aikatar noma saboda caccakar gwamnatin El-Rufai da ya saba yi.

An rantsar da sauran 13 cikin murna da farin ciki a fadar gwamnatin jihar Kaduna.

Kwamishinonin da aka rantsar sun hada da: Ja’afaru Ibrahim Sani, ma’aikatar da ke kula da harkokin karamar hukuma; Idris Samaila Nyam, Ma’aikatar kasuwanci, kirkire-kirkire da fasaha; Shehu Usman Makarfi, Ma’aikatar ilimi; Ibrahim Garba Hussaini, M’aikatar muhalli da ma’adinai; Kabir Muhammad Mato, Ma’aikatar ci gaban wasanni; Balaraba Aliyu-Inuwa, Ma’aikatar ayyukan jama’a da ababen more rayuwa da kuma Samuel Peter Aruwan, Ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida.

KU KARANTA KUMA: Shan kayan zaki na janyo cutar daji - Bincike

Sauran sun hada da: Fausat Adebola Ibikunle, Ma’aikatar gidaje da ci gaban birane; Mohammed Bashir Saidu, Ma’aikatar kudi; Hafsat Mohammed Baba, Ma’aikatar ci gaban jama’a; Aisha Dikko, Ma’aikatar shari’a; Mista Thomas Gyang, Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi; Alhaji Hassan Mahmud, kwamishina a ofishin gwamna kan zanga-zanga, barna da gyara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel