Buhari ya bayar da N5bn kudin tallafi ga Kwamitin bincike mai zurfi na TETFund

Buhari ya bayar da N5bn kudin tallafi ga Kwamitin bincike mai zurfi na TETFund

-Buhari ya ba da N5bn ga Kwamitin gudanar da bincike mai zurfi na TETFund a matsayin kudin tallafi

-Shugaban TETFund, Farfesa Bogoro ne ya bada wannan sanarwar ranar Alhamis Abuja wurin bikin kaddamar da Kwamitin binciken

-Shugaban wannan kwamiti a nasa bangaren yace a shirye yake da gudanar da wannan aiki da aka daura masa

Shugaba Muhammadu Buhari ya aminta da bayar da N5bn ga Kungiyar makarantun gaba da sakandare wato (TETFund) domin bunkasa yin bincike mai zurfi wanda zai kawo cigaban Najeriya.

Shugaban TETFund, Farfesa Elias Bogoro ne ya bada wannan sanarwar a wurin bikin kaddamar da Kwamitin gudanar da bincike mai zurfi a Abuja ranar Alhamis.

KU KARANTA:Zaben 2019: Yau Atiku zai gabatar da bidiyo matsayin shaida a kotu

A cewar shugaban, kwamitin zai maida hankali ne a fannin gudanar da bincike mai zurfi a aikace wadanda ke da matuqar amfani da kuma buqatar tallafin kudi domin a samu damar aiwatar dasu.

Ya buqaci kwamitin da su fito da ayyuka masu muhimmanci wadanda za’a iya daukar nauyinsu ta hanyar samar da kudaden yinsu.

A na shi jawabin na godiya, Shugaban Kwamitin, Farfesa Olufemi Bamiro yayi alkawarin cewa zai yi aiki tukuru domin bai wa masu yin bincike mai zurfin damar samun tallafin da suke da buqata.

A wani labarin mai kama da wannan, zaku ji cewa, a yau ne Atiku Abubakar zai gabatar da wani bidiyo mai kunshe da sahidu kan magudin zaben da yake ikirarin cewa APC dad an takararta Muhammadu Buhari sun gudanar a lokacin zaben 23 ga watan Fabrairu.

A mako mai zuwa ne ake sa ran Atiku da PDP za su gabatar da shaidarsu ta karshe wadda kuma ita ce zata kasance sha kundum dukkanin shaidun nasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel