Tashin hankali: Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 16

Tashin hankali: Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 16

Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 16 a yankin Rumuji – Elele da ke a yankin Kudu maso Yamma a jihar Rivers.

Wadanda aka sace sun kasance matafiya daga tashar Ekeki a Yenagoa, babbar birnin jihar Bayelsa zuwa Port Harcourt, jihar Rivers, a lokacin da aka tsare motar nasu sai masu garkuwar suka tisa keyarsu zuwa cikin daji.

Kakakin rundunar yan sanda reshen ihar Rivers, DSP Nnamdi Omoni, wanda ya tabbatar ma tashar Channels TV afkuwar lamarin, yace an soma farautar yan bindigan kuma ana kokarin kubutar da wadanda aka sace.

“Muna sane da ayyukan yan bindiga a hanyar Kudu maso Gabas, muna iya kokarinmu don ganin mun magance lamarin, musamman lamarin garkuwa da mutane.

“Mun fara farautar masu garkuwa da mutanen sannan ana kokarin ganin an ceto mutanen da aka sace.”

KU KARANTA KUMA: Yan Abuja sun ba gwamnatin tarayya awa 48 ta kawo karshen zanga-zangar yan shi’a

A wani labarn kuma, mun ji cewa wasu 'yan sanda da aka tura domin kawo karshen matsalar masu garkuwa da mutane akan babbar hanyar Ife zuwa Ibadan, a yankin kudu maso yammacin Najeriya, an kama su ranar Litinin dinnan da ta gabata suna tare motoci.

'Yan sandan wadanda suke aiki akan hanyar Ibadan, Ikire, Gbongan da kuma Ile-Ife, sun tare wata mota wacce wakilin jaridar Premium Times yake ciki dauke da fasinjoji 17, inda suka nemi a basu cin hanci kafin su kyale motar ta wuce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel