Buhari bai taba neman alfarma daga NNPC ba, baya sanya baki a abubuwan da muke yi - Kyari

Buhari bai taba neman alfarma daga NNPC ba, baya sanya baki a abubuwan da muke yi - Kyari

- Babban manajan darakta na kamfanin man fetur a Najeriya (NNPC), Mista Mele Kyari ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba neman alfarma daga kamfanin ba

- Kyari ya kuma bayyana cewa shugaban kasar baya sanya masubaki a abubuwan da suke yi

- Ya kuma bayyana cwa za su yi aiki cikin gaskiya da amana

Sabon babban manajan darakta na kamfanin man fetur a Najeriya (NNPC), Mista Mele Kyari a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba neman alfarma ba daga kamfanin tun daga lokacin da aka zabe shi a 2015.

Har ila yau yace kaamfanin NNPC ta jajirce wajen amincewa da hadin gwiwar Gwamnati.

Kyari ya bayyana jawabin ne a wani tataunawa da suka yi a taron bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa na Afrika karo na uku wanda aka gudanar a Abuja wanda hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta shirya.

Yace: "Suhgaban kasar bai taba neman alfarma ba daga kamfaninmu kuna baya saka baki cikin yanda muke gudanar da ayyukanmu. Za mu yi iya bakin kokarinmu mu kasance masu gaskiya da amana."

KU KARANTA KUMA: Yan Abuja sun ba gwamnatin tarayya awa 48 ta kawo karshen zanga-zangar yan shi’a

Kyari wanda ya jagoranci tawagar mutane 11 zuwa taron yace: “NNPC ta kasance hukumar dake mayar da hankali wajen hadin gwaiwar Gwamnati. Zamu tabbatar mun bayyana duk ayyukan da muke gudanarwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel