Dalilin da yasa na kasa aiwatar da rahoton taron kasa na 2014 - Jonathan

Dalilin da yasa na kasa aiwatar da rahoton taron kasa na 2014 - Jonathan

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan, a ranar Alhamis ya ce lokaci ya yi da za a jingine banbance-banbancen siyasa a aiwatar da shawarwarin da ke cikin rahoton taron kasa da aka gudanar a shekarar 2014 a zamanin mulkinsa.

Ya ce gwamnatinsa ba ta samu ikon aiwatar da shawarwarin zaben bane saboda kurewar lokaci duba da cewa daf da zaben 2015 aka mika masa rahoton.

Jonathan ya yi wannan jawabin ne a wurin taron kaddamar da wani littafi mai shafuka 669 da aka yi wa lakabi da “The Dream: Pursuing the Black Renaissance through the Murky Waters of Nigerian Politics,” da fittacen dan siyasa Sanata Femi Okurounmu ya rubuta.

DUBA WANNAN: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

Jonathan wanda ya sha kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2015 ya ce za a magance mafi yawancin matsalolin da ke adabar Najeriya idan aka aiwatar da shawarwarin da ke rahoton taron kasar na 2014.

"Nayi imanin cewa za mu samu hanyoyin wareware matsalolin da muke fama da su a yau idan aka aiwatar da shawarwarin da aka bayar yayin taron kasa na 2014.

"Idan muka dena jefa siyasa cikin lamaran kasar nan, akwai yiwuwar kaddamar da shawarwarin da kwamitin taron kasar ta bayar za su warware matsalolin kasar," inji Jonathan.

Tsohon shugaban kasan kuma ya bukaci a canja tsarin yadda ake nada Shugaban INEC da sauraan mambobin hukumar domin samun zabe masu inganci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel