Tirkashi: Wasu 'yan sanda da aka tura su yaki masu garkuwa da mutane, sun buge da karbar cin hanci a hannun direbobi

Tirkashi: Wasu 'yan sanda da aka tura su yaki masu garkuwa da mutane, sun buge da karbar cin hanci a hannun direbobi

- Wasu jami'an 'yan sanda da aka tura su yaki masu garkuwa da mutane sun buge da karbar cin hanci a hannun direbobi

- Hakan ya biyo bayan komawa kan manyan hanyoyin Ile-Ife da Ibadan suna tare motocin direbobi suna karbar cin hanci kafin su barsu su wuce

- Hnayoyin dai sun yi kaurin suna wurin masu garkuwa da mutane da kuma 'yan fashi da makaki, wadanda suka mayar da ita wurin baje kolin ta'addancin su

Wasu 'yan sanda da aka tura domin kawo karshen matsalar masu garkuwa da mutane akan babbar hanyar Ife zuwa Ibadan, a yankin kudu maso yammacin Najeriya, an kama su ranar Litinin dinnan da ta gabata suna tare motoci.

'Yan sandan wadanda suke aiki akan hanyar Ibadan, Ikire, Gbongan da kuma Ile-Ife, sun tare wata mota wacce wakilin jaridar Premium Times yake ciki dauke da fasinjoji 17, inda suka nemi a basu cin hanci kafin su kyale motar ta wuce.

Wasu daga cikin direbobin da suka yi magana da wakilin Premium Times sun tabbatar da cewar 'yan sandan suna karbar cin hanci, kuma abin yayi tsamari ma, bayan da 'yan sandan suka sanya shinge akan hanyar wucewar.

KU KARANTA: Za a sayar da wasikar da Tupac ya rubutawa Madonna domin su rabu akan kudi naira miliyan 108

Wani jami'in dan sanda dake kan hanyar Gbongan, mai suna Akosoba A kamar yadda aka sanya a jikin kakinshi, ya karbi naira 100 daga gurin wani direba, sannan ya mayar masa da canjin naira 50.

Haka kuma wani dan sanda akan hanyar Ile-Ife, ya umarci wani direba ya tsaya domin ya bincike shi, amma yana sunna masa naira 50 sai ya bashi hannu ya wuce.

Su dai wadannan 'yan sanda an tura su wannan yankin ne domin su sanya ido akan masu garkuwa da mutane da suka addabi matafiya da suke bin wannan manyan hanyoyi.

A cikin watanni uku da suka gabata an sace mutane masu dumbin yawa tare da kashe wasu wadanda basu ji ba basu gani akan wannan hanyoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel