An sake damke yan Shi'a 65 a Abuja

An sake damke yan Shi'a 65 a Abuja

Hukumar yan sanda ta sake garkame mabiyar akidar Shi'a 65 a sabuwar zanga-zanga da suka gudanar da matattarar ma'aikatun gwamnati dake birnin tarayya Abuja.

Mabiya El-Zakzaky sun koma zanga-zanga ne bayan batakashin da ya faru tsakaninsu da jami'an yan sanda a majalisar dokokin tarayya inda suka jikkata jami'an yan sanda da lalata motocin jama'a ranar Talata.

Game da cewar kwamishanan yan sandan birnin tarayya, Bala Ciroma, wanda yayi magana da manema labarai, wadanda aka damke zasu gurfana gaban kotu.

Jami'an yan sanda sun watsawa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa domin tarwatsasu kuma hakan ya tayar da kura.

KU KARANTA: Yau Kotu za ta yanke hukunci a tuhumar da ake yi ma shugaba Buhari

A bangare guda, Mabiya Shia sun fara gangamin zanga zanga a garin Kaduna, kamar yadda suka yi a babban birnin tarayya Abuja, da kuma jahar Legas, a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan shian sun fara zanga zangar ne da misalin karfe 2 na rana a kan titin Jos dake cikin gari, amma kafin a ankara sun mamaye titunan Kano da kuma Kontagora har ma babbar kasuwar garin Kaduna.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa yan Shi’an suna gudanar da zanga zangar ne don nuna bacin ransu da cigaba da rike jagoransu Malam Ibrahim Zakzaky da gwamnatin Najeriya ta kama tun shekaru 4 da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel