Yanzu-yanzu: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki dakin kwanan dalibai mata a UI

Yanzu-yanzu: 'Yan fashi da makami sun kai farmaki dakin kwanan dalibai mata a UI

'Yan fashi da makami sun afka dakin kwanan dalibai mata ta Obafemi Awolowo da ke Jami'ar Ibadan (UI) a daren ranar Alhamis 11 ga watan Yulin shekarar 2019.

A cewar wadanda abin ya faru a idanunsu, 'yan fashin da adadin su ya kai 10 sun kwashe kimanin sa'o'i biyu suna cin karen su ba babbaka.

Masu kula da dakin kwanan sunyi kammala zagaye a wasu dakunnan misalin karfe 11 na dare amma daga baya daliban suka ji karar buga kofa kuma suka bude domin suna tsamanin masu kula da su ne suka dawo.

DUBA WANNAN: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

Budewarsu ke da wuya sai 'yan fashi da makamin suka shigo dakin kwanan cikin sauki.

'Yan fashi da makamin sun raunatta a kalla dalibai biyar yayin da suka sace wayoyin salula da komfuta (laptops) masu yawa daga hannun daliban.

Jami'in Hulda Da Jama'a na Jami'ar, Mista Olatunji Oladejo ya tabbatar da afkuwar lamarin a hirar tarho da ya yi da The Punch.

Olatunji ya ce, "Mummunan lamarin ya faru ne misalin karfe 1.30 na dare yayin da wasu maza 10 dauke da bindigu suka afka dakin kwanan dalibai mata. Dalibai biyu da suka jikkata suna asibitin Jaja suna karbar magani.

"Jami'an tsaro na Jami'ar mu da 'Yan sanda daga Bodija, Sango da Ojoo da Operation Burst sun garzaya wurin amma 'yan fashin sun tsere."

Ya ce an fara bincike domin gano 'yan fashin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel