Yan daba 500 sun mika makamansu ga gwamnatin jihar Bauchi

Yan daba 500 sun mika makamansu ga gwamnatin jihar Bauchi

-Fiye da mutane 500 ne na yan kungiyar ta’addanci suka mika wuya a jihar Bauchi

-Komishinan yan sanda na jihar, Habu Sani ya bayyana cewa mafi yawan yan sara sukan matasa ne ma su hazaka da za su bayar da gudunmuwa idana aka kula da su

-Komishinan ya yi kira ga gwamnatin jihar da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen inganta rayuwar matasan

Fiye da mutane 500 ne na yan kungiyar ta’addanci da aka fi sani da ‘Sara Suka’ suka mika wuya suka yadda makamansu a jihar Bauchi.

Tubabbun yan ta’addan, wanda duk matasa ne masu shekaru daga 18 zuwa 25 sun bayar da makamansu da suka hada da wukake, adduna da gariyo da kuma bindigogin hannu a wajen taron da aka gudanar a hedikwatar yan sanda ta jihar Bauchi.

Da yake magana a wajen taron, komishinan yan sanda na jihar, Habu Sani ya bayyana cewa an samu wannan ci gaba ne sakamakon matsi da aka sanya ma yan ta’addan da kuma gangamin da rundunar ke shiryawa akan wayar da kan jama’a game da illolin ta’addanci da shaye shaye.

Ya bayyana cewa “Fiye da yan daba 500 suka mika wuya suka tuba daga wannan ta’addancin a jihar. Mafi yawan matasan da ke wanna ta'addanci na sara suka masu hazaka ne kuma za su bayar da gudunmuwa sosai idan aka kula da su.”

KARANTA WANNAN: In zaka fadi fadi gaskiya: An karrama sheikh Ahmad Gumi saboda fadar gaskiyarsa

Ya bayyana cewa mutum 294 a cikin su na da sana’ar hannu, 31 da cikinsu dalibai, sa’annan 170 ne ba su da abin yi.

Daga karshe komishinan ya yi kira ga gwamnatin jihar da kungiyoyi masu zaman kansu da su tallafa wajen ganin an kubuto matasan daga cikin halin da suka shiga don a daidaita su zuwa hanya madaidaiciya.

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata na gidan gwamnati, Abubakar Kari, yayi alkawarin inganta rayuwar al’ummar jihar Bauchi.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel