Gwamnan Jigawa yayi magana da kakkausar murya akan dakatar da shirin Ruga

Gwamnan Jigawa yayi magana da kakkausar murya akan dakatar da shirin Ruga

-Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bada tabbacin cewa an dakatar da shirin samar da Ruga ne ga makiyaya har zuwa lokacin da za a gama sanya duk matakan da suka dace

-Gwamnan jihar Jigawan ya kuma kara jaddada cewa samar da Ruga hakki ne ga makiyaya ba wai alfarma ba

-Badaru ya bayyana cewa wajajen zama na Ruga ko wajajen da aka kebe na kiwon wani shiri ne da zai inganta harkar kiwo a Najeriya

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya kara jaddada cewa an dakatar da shirin samar da Ruga ga makiyaya har zuwa lokacin da za a kammala wasu tsare tsare.

Gwamnan ya bayyana cewa wajajen zama na Ruga da wajajen kiwon, ko ma dai mi nene, shiri ne wanda zai inganata al’umma da wadanda suke kasuwanci, kai har ma da shugabanci.

Gwamna Badaru ya kuma jaddada cewa shirin samar da wajajen zama na Ruga hakki ne ga makiyaya ba wai alfarma ba.

Ya bayyana cewa kasuwancin kiwo kasuwanci ne mai kyau da doka ta yadda da shi, a saboda haka hakkin makiyaya ne gwamnati ta tallafa masu, ta samar masu da wurare masu kyau da za su yi kasuwancinsu ba tare da kabilanci ba, saboda hakkinsu ne ba wai alfarma ba ce za a yi masu.

KATANTA WANNAN: Kwararru kuma amintattu kadai zan nada ministoci a gwamnatina, Inji Buhari

Gwamnan ya bayyana cewa samar da wajajen zama na Ruga da wajajen kiwo wani shiri ne na gwamnatin tarayya da zai inganta harkar kiwo ta yadda masu kasuwancin za su yi shi cikin tsafta, cikin zaman lafiya da lumana sa’annan kuma ya habbaka ribar kasuwancin.

Gwamnan ya bayyana cewa yan kasuwa na cikin gida da na kasashen waje na so su zuba hannun jari a kasuwancin kiwo saboda ya na daya daga cikin kudirorin gwamnatin tarayya na yin kasuwanci cikin sauki

Ya kara da cewa kasuwancin kiwo na samar wa da miliyoyin mutane sana’a da za su kula da kansu da ilayansu, sa’annan ya na samar da abinci da kuma kudaden shiga ga gwamnatin tarayya.

Ya bayyana cewa “Gwamnatin tarayya ba ta soke shirin samar da Ruga ba, an dakatar da shi ne kawai don sake duba tsari kuma za a tabbatar da shi don ci gaban duka yan Najeriya ba wai masu kiwo kawai ba.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel