Ka fada ma Buhari ya saki Zakzaky – Yan shi’a ga Tinubu

Ka fada ma Buhari ya saki Zakzaky – Yan shi’a ga Tinubu

- Mambobin kungiyar Musulmai na Shi’a, sun bukaci babban jigon AAPC na kasa da ya fa ma Buhari cewa ya saki shugabansu

- Yan shi’an sun bayyana cewa a shirye suke su mutu har sai an saki shugabansu

- Acewar kungiyar, suna da rayuka miliyan 21 da za sub a hukumomin tsaro a cci gaba da bukatarsu na a saki El-Zakzaky

Kungiyar yan shi’a sun yi kira ga babban jigon jam’iyyar the All progressives Congress, Bola Tinubu, da ya fada ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewar ya saki shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky.

Mambobin kungiyar na shi’a yayinda suke zanga-zangar ci gaba da tsare El-Zakzaky, sun bayyana cewa a shirye suke da su mutu har sai an saki Shugaban nasu.

Da yake Magana a madadin kungiyar, jagoran kungiyar a kudu maso yamma, Muftau Zakariya, a lokacin zanga-zangar a Lagas, yace kungiyar na da rayuka miliyan 21 da za su bayar a bukatarsu na a saki El-Zakzaky.

KU KARANTA KUMA: Ban ce Buhari zai gabatar da sunayen ministoci a wannan makon ba – Lawan

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa an sake samun salwantar rai a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli yayin zanga-zangar mabiya kungiyar shi’a da ke neman a saki shugabansu, Malam El-Zakzaky a jihar Kaduna.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa mabiya kungiyar sun tabbatar da cewar an kashe masu mutum daya mai suna Ahmad a wajen zanga-zangar da suka gudanar a yau Alhamis.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel