Kwararru kuma amintattu kadai zan nada ministoci a gwamnatina, Inji Buhari

Kwararru kuma amintattu kadai zan nada ministoci a gwamnatina, Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana irin mutanen da yake muradin nadawa a mukamin ministoci a sabuwar gwamnatinsa, inda yace kwararru kuma amintattu kadai zai nada.

Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne daren Juma’a yayin da ya karbi bakuncin shuwagabannin majalisar dokokin Najeriya a wata liyafar cin abinci daya shirya musu a fadar gwamnati, Aso Rock Villa.

KU KARANTA: Ba zamu lamunci karin farashin man fetir ba – PDP ta gargadi Buhari

A jawabinsa, Buhari yace yana fuskantar matsin lamba daga bangarori daban daban akan nadin sabbin ministoci, amma yace duk da matsin lambar, mutanen dake da inganci, kwararru kuma amintattu kadai zai nada.

Kwararru kuma amintattu kadai zan nada ministoci a gwamnatina, Inji Buhari

Buhari da yan majalisa
Source: Facebook

“Na san mutane da dama a taron nan sun kosa su ga sunayen wadanda zan nada ministoci domin hankalinsu ya kwanta, ina fuskantar matsin lamba akan haka, amma a cikin tsofaffin ministocina ban san dayawa daga cikinsu ba.

“Na dai karbesu ne daga jam’iyyarmu da kuma wasu mutanena, amma da nayi aiki dasu na tsawon shekaru 3 da rabi, muna haduwa akalla sai biyu a wata, a haka na sansu, amma a yanzu zan bi a hankali na zabo wadanda na sani da kaina.” Inji shi.

Daga karshe Buhari ya bukaci majalisar dokokin Najeriya ta hada hannu da bangaren zartarwa wajen samar da ingantaccen dangantaka da zai haifar da cigaba mai daurewa a Najeriya, musamman a zangon mulkinsa na karshe.

Da yake nasa jawabin, Sanata Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa ya musanta batun da ake yadawa na cewa wai yace shugaban kasa zai mika musu sunayen sabbin ministocinsa cikin wannan sati.

Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanat Ovie Omo-Agege, kaakakin majalisa Femi Gbajabiamila, mataimakin kaakakin majalisa Ahmed Idris Wase, shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da sauran shuwagabannin majalisa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel