Ban ce Buhari zai gabatar da sunayen ministoci a wannan makon ba – Lawan

Ban ce Buhari zai gabatar da sunayen ministoci a wannan makon ba – Lawan

- Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan yace bai taba fadin cewaa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da suneyen ministoci ga majalisar dattawa a wannan makon ba

- Shugaban majalisar dattawan ya yi nuni ga cewa abunda ya fadi shine cewa za a iya samun sunayen a wannan makon

- Lawan y bukaci yan jarida da su dunga kawo rahoton lamari yadda yake

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya caccaki rahoton kafofin watsa labarai da aka kawo cewaa shi yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da jerin sunayen ministoci a majalisar dattawa a wannan makon.

Lawan ya yi karin haske a wata hira da manema labarai na fadar Shugaban kasa a ranar Alhamis, 11 ga Yuli bayan wata ganawa tare da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, NAN ta ruwaito.

Shugaban majalisar dattawan ya yi nuni ga cewa abunda ya fadi shine cewa za a iya samun sunayen a wannan makon.

Sauran wadanda suka halarci ganawar sun hada da mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege; kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Ahmed Idris Wase.

KU KARANTA KUMA: Da zafi-zafi: Shugaba Buhari na cikin ganawa da shugabannin majalisar dokokin kasar

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Comrade Adams Oshiomhole, da sauran hadiman Shugaban kasa ma duk sun halarci ganawar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel