Ba zamu lamunci karin farashin man fetir ba – PDP ta gargadi Buhari

Ba zamu lamunci karin farashin man fetir ba – PDP ta gargadi Buhari

Babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya, PDP, ta gargadi shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC mai mulki da kada su kuskura su kara farashin man fetir a halin da ake ciki, domin kuwa ba zata lamunta.

PDP ta bayyana haka ne ta baki kaakakinta, Kola Ologbondiyan a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli inda ta ce ta dauki wannan matsayi ne kamar yadda aka santa da manufar kyautatawa tare da inganta walwalar yan Najeriya.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta bankado naira miliyan dubu 3 da wasu mutane 2 suka boye a banki

Jam’iyyar tace duk wani karin farashin man fetir zai janyo tashin gwauron zabi akan farashin kayayyakin abinci, dana masarufi a kasuwanni da sauran abubuwa, wanda hakan zai kara tsananta mawuyacin halin da yan Najeriya ke ciki a yanzu.

“A irin wannan lokaci da yan Najeriya ke cikin matsi, a maimakon kara fatashin man fetir, kamata yayi gwamnati idan tana da hankali ta tuntubi masu ruwa da tsaki don neman mafita tare da rage farashin man fetir ko yan Najeriya zasu samu sa’ida.

“Don haka ba zamu lamunci karin farashin man fetir ba, hakan ya nuna jam’iyyar APC muguwa ce, mai son kai, wanda bata damu da halin yan Najeriya ke ciki ba, asali ma tana jin dadin jefa yan Najeriya cikin mawuyacin hali.

“Idan ba shuwagabannin da basa kaunar yan Najeriya ba wanene zai yi tunanin kara farashin man fetir a wannan lokaci, sai dai shuwagabannin da suke ganin babu wanda ya isa ya tambayesu yadda suke gudanar da mulki.” Inji PDP.

Daga karshe PDP ta yi da na sanin zaben Buhari a matsayin shugaban kasa da yan Najeriya suka yi, inda tace da yanzu yan Najeriya suna cin gajiyar tsarin tattalin arziki da Atiku Abubakar ya shirya da ace sun zabeshi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel