Ta faru ta kare: Muna ji muna gani jami'an tsaro suka kore mu daga wajen hada sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 - Jami'in PDP Adam

Ta faru ta kare: Muna ji muna gani jami'an tsaro suka kore mu daga wajen hada sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 - Jami'in PDP Adam

- Wani jami'in hukumar zabe ya bayyana yadda tashin bam ya kawo matsala gurin hada sakamakon zabe a jihar Borno.

- Ya bayyana cewa ranar da za a gabatar da zabe babu wanda ya fito wajen zabe saboda tashin wannan bam din da ya faru a karamar hukumar

- Ya kara da cewa daga baya ma jami'an tsaro ne suka kore su daga wajen hada sakamakon zaben shugaban kasar na karamar hukumar

Ranar Alhamis din nan ne Adam Ali Hamsami ya rantse a gaban kotun sauraron kararrakin zabe ta kasa akan cewa sau biyar bam tashi a karamar hukumar Jere da misalin 12 na dare da kuma safiyar ranar 23 ga watan Fabrairu.

"An kai hari Hadamari da Gongolon, mutane duka suka gudu cikin garin Maiduguri don tsira da rayuwarsu," in ji shi.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An cimma yarjejeniya tsakanin manyan makarantun kasar waje da Engr. Rabiu Musa Kwankwaso

Hamsami ya kara da cewa a matsayinsa na jami'in kula da zabe na jam'iyyar PDP a yankin, yayi kokari wurin ganin ya hado kan wasu jami'an jam'iyyarsa domin su dawo wajen zaben.

Ya ce ya samu rahoto daga gurin daya daga cikin jami'an jam'iyyar cewa mutane sunki fitowa zabe saboda babu jami'an hukumar zabe a wuraren zaben.

Ya kara da cewa jami'an tsaro ne suka kori jami'an jam'iyyar PDP daga wajen da ake hada sakamakon zabe na karamar hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel