Gwamnatin Buhari ta bankado naira miliyan dubu 3 da wasu mutane 2 suka boye a banki

Gwamnatin Buhari ta bankado naira miliyan dubu 3 da wasu mutane 2 suka boye a banki

A cigaba da yaki da rashawa, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu ta sake samun nasara, inda ta bankado wasu tarin asusun bankuna dake makare da biliyoyin nairori mallakin wasu manyan ma’aikatan gwamnati guda biyu.

Kwamiti na musamman da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa domin kwato kudaden sata daga hannun tsofaffin jami’an gwamnati da yan siyasa ce ta samu nasarar bankado makudan kudaden da suka kai naira biliyan 3 daga hannun Aisha Usman da Goody Nnaji.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Yan Shia sun gudanar da zanga zanga a garin Kaduna

Gwamnatin Buhari ta bankado naira miliyan dubu 3 da wasu mutane 2 suka boye a banki

Aisha da Nnaji
Source: Facebook

Shugaban kwamitin, Okoi Obono-Obla ne ya sanar da haka a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli yayin da yake ganawa da manema labaru a Abuja, inda yace Goody Nnaji da Aisha Usman ma’aikata ne a hukumar daidaita kundin man fetir, watau Petroleum Equalization Fund.

Mista Obla yace Aisha ce babbar manajan ayyuka a hukumar, yayin da shi kuma Nnaji yake rike da mukamain manajan hulda da jama’a, kuma a yanzu haka yana halartar kwas a cibiyar tsare tsare ta kasa dake Kuru, jahar Filato.

Majiyarmu ta ruwaito Obla yana cewa: “Mun samu korafi daga wasu mutane dake nuna cewa Nnaji ya bude wani asusun banki da sunan Otal dinsa mai suna Galbani and GreatWood a garin Owerri na jahar Imo da muka bincika sai muka tarar daga shekarar 2011 zuwa 2019 an saka naira 2.2billion, dala 302,964, Yiro 11,000 da pan 2,000.

“Da kuma takardun kadarori da gidaje, an kama shi, kuma ya sha tambayoyi, amma daga bisani aka bada belinsa, Ita kuma Aisha mun sameta ne da naira biliyan 1.4 a asusun banki guda 9, kuma duk na banki daya.” Inji shi.

Sai dai Obla yace kamar wasu kamfanoni masu zaman kansu ne suka antaya mata wadannan kudade, musamman kamfanonin man fetir da suke taimakamawa wajen samun izinin hakar mai, daga karshe yace sun gayyaci wasu ma’aikatan hukumar domin su bincikesu, kafin su gurfanar da Nnadi da Aisha gaban kotu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel