Zaben 2019: Yau Atiku zai gabatar da bidiyo matsayin shaida a kotu

Zaben 2019: Yau Atiku zai gabatar da bidiyo matsayin shaida a kotu

-Atiku zai gabatar da wata muhimmiyar shaida a kotun zaben shugaban kasa

-Atiku da jam'iyyarsa ta PDP sun shirya tsaf domin kunna wa kotun zaben bidiyo wanda a cewar wakiliansu a kotu yana dauke da yadda APC ta tafka magudin zabe

-A cikin mako mai zuwa PDP da Atiku ke shirin kammala karar tasu inda zasu gabbatar da wata babbar shaida a kotun

Jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar za su gabatar da bidiyo a matsayin shaida kan zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu a kotun zabe dake Abuja yau din nan.

Wani babban lauya daga cikin tawagar lauyoyin Atikun ne ya bada wannan bayani, inda yake cewa cikin bidiyon da za su kawo kotu, za’a ga yadda APC ta tafka magudi a lokacin da ake kada kuri’u.

KU KARANTA:Jerin sunayen sabbin hadiman Kakakin Majalisar wakilai su 6

Har ila yau, a cikin mako mai zuwa ne ake sa ran Atiku da jam’iyyar PDP za su gabatar da babbar shaida kuma ta karshe a gaban kotun yayin da za su kammala karar da suka shigar ta kalubalantar zaben shugaban kasan da ya gabata.

Bugu da kari, tawagar lauyoyin ta kira wasu jami’an zabe masu tattara sakamako a matakin kananan hukumomi guda tara a matsayin shaidu, wadanda suka bada shaida a kan muzgunawa ga masu zabe, soke sakamakon zabe da kuma cin zarafin masu kada kuri’a.

Daya daga cikin jami’an mai suna, Adam Ali Hamsami ya bada jawabi a kan tashin bam har sau biyar a karamar hukumar Jere da misalin karfe 12 na daren Asabar, 23 ga watan Fabrairu ranar da ake sa ran za’a tashi da zabe da safe.

A cewar Hamsami, “ Tashin bam din ya kawo cikas a cibiyoyin tattara sakamako masu yawa dake Borno. Akwai hari da aka kai Hadamari da Gongolon inda jama’ar wurin suka gudu zuwa Maiduguri.”

A jawabin daya daga cikin lauyoyin APC, Dipo Okpeseyi (SAN) ya ce: “ An samu tsaiko ne a wadannan wuraren saboda malaman zabe basu kawo kayayyakin zabe da wuri ba kamar yadda aka tsara.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel