INEC ta fara shirin babban zaben kasa na 2023 - Yakubu

INEC ta fara shirin babban zaben kasa na 2023 - Yakubu

Farfesa Mahmoud Yakubu, shugaban hukumar zabe ta kasa mai zamanta, INEC, ya ce hukumar ta fara shiri a kan babban zaben kasa na 2023 yayin ci gaba da ake ci gaba da gudanar da bita daki-daki kan zaben kasa da ya gudana a bana.

Shugaban hukumar INEC ya bayar da shaidar hakan a ranar Alhamis 11, ga watan Yulin 2019, yayin taron bitan babban zaben kasa na 2019 da aka gudanar tare da kwamishinonin hukumar a birnin Ikeja na jihar Legas.

A yayin wannan taro da ya kasance na 12 cikin jerin tarukan bitan zaben 2019 da hukumar INEC ke ci gaba da gudanarwa, Farfesa Yakubu ya sha alwashin inganta harkokin gudanarwa a babban zabe na 2023.

Kamar yadda hukumar INEC ta sha alwashi, ta na ci gaba da bitan zaben 2019 domin dinke baraka wajen gano kurakurai da tayi a baya tare da daukar izina na gyara duk wani nakasu da take da shi gabanin tunkarar babban zaben kasa na gaba.

KARANTA KUMA: Buhari ya nemi amincewar majalisar dattawa a kan sake nadin wasu hadiman sa 15

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, hukumar INEC na ci gaba da gudanar da taruka daban-daban cikin tsawon watanni biyu da suka gabata a garin Abuja da kuma jihar Legas. INEC tare da dukkanin masu ruwa da tsaki na bitan yadda zaben kasa ya gudana cikin kananan hukumomi 774 da kasar nan ta kunsa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel