‘Yan sanda, Majalisar dokoki da Ma’aikatar Shari’a na kan gaba cikin hukumomin da suka fi kowa cin hanci da rashawa a Najeriya – Hasashe

‘Yan sanda, Majalisar dokoki da Ma’aikatar Shari’a na kan gaba cikin hukumomin da suka fi kowa cin hanci da rashawa a Najeriya – Hasashe

-Hasashen wata kungiya mai suna Transparency International ta bayyana sunayen hukumomin dake kan gaba wurin cin hanci da rashawa a Najeriya

-A cewar wannan kungiya hukumar 'yan sanda ita ce a mataki na farko da kashi 69% sai kuma Majalisar dokoki a mataki na biyu da kashi 60%

-An samu wannan sakamakon ne daga zaben jama'a bisa ra'ayoyinsu a kan lamarin cin hanci da rashawa kamar yadda kungiyar ta bamu labari

A ranar Alhamis ne kungiyar Transparency International ta bayyana sunayen hukumomi guda uku wadanda ke kan gaba wurin mu’amala da cin hanci da rashawa.

Wadannan hukumomin dai su ne: ‘Yan sanda, Majalisar dokoki da kuma Ma’aikatar Shari’a. Wannan kungiyar ta sanya wa binciken nata taken ‘ Ma’aunin cin hanci a yankin Afirka na shekarar 2019: Ra’ayoyin jama’a game da cin hancin.’ Wannan shirin shi ne kashi na goma a jerin ire-irensa.

KU KARANTA:Jerin sunayen sabbin hadiman Kakakin Majalisar wakilai su 6

A cewar Transperancy International, cin hanci da rashawa babbar matsalace wadda ke kawo tafiyar hawainiya a bangaren cigaban tattalin arziki da kuma siyasar Afirka.

“ Babbar matsalace ga cigaban tattalin arziki, kyakkyawan shugabanci, yancin fadin ra’ayinka da kuma ‘yancin kalubalantar gwamnati a kan kusakuranta.

“ Kari a kan wannan, cin hanci da rashawa yana haifar da takura da kuma rashin jin dadi a rayuwar al’umma. A yayin da lamarin yake daukar sabon salo daga kasa zuwa kasa, ma’aikata zuwa ma’aikata, cin hanci na tafka babbar illa ga miliyoyin mutane wadanda ke rasa samun rayuwa mai inganci.

“ Wannan shirin namu mai taken ‘Global Corruption Barometer- Africa’ a turance, shi ne irinsa kasha na goma. Kuma shirin na wannan lokaci ya mayar da hankali ne a kan wuraren da matsalar cin hanci da rashawan ta fi shafa.

Kimanin 69% na wadanda suka sanya hannu cikin has ashen sun lafta hannu kan hukumar ‘yan sanda a matsaiyin hukuma da tafi ko wacce cin hanci, 60% kuma suka zabi Majalisar dokoki a yayinda kashi 51% suka zabi alkalai da ma’aikatar shari’a.” Kamar yadda hasashen ya bayyanawa jaridar Premium Times.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel