Abdulsalami ya bayyana babban abinda ke haddasa matsalar rashin tsaro a Najeriya

Abdulsalami ya bayyana babban abinda ke haddasa matsalar rashin tsaro a Najeriya

Tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar ya ce za a cigaba da fuskantar kallubalen tsaro a Najeriya saboda mafi yawancin 'yan Najeriya ba su da aikin yi.

A cewar Abubakar, rashin samar da ayyukan yi da kuma rashin karfin tattalin arziki a kasar ne ya haifar da garkuwa da mutane, ta'addanci, fashi da makami da sauran ayyukan laifi da gwamnati mai ci yanzu ke fama da shi.

A jawabin da ya yi bayan ziyarar da ya kai wa Gwamna Seyi Makinde a ofishinsa da ke Ibadan, Abubakar ya jadada cewa ya zama dole gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta inganta tattalin arziki kuma ta nemi hadin kan 'yan Najeriya wurin magance matsalolin tsaro.

DUBA WANNAN: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

Bugu da kari, ya kuma ce akwai bukatar 'yan Najeriya su rika taimakawa gwamnati wurin samar da tsaro ta hanyar bayar da bayyanan sirri duk lokacin da suka lura da afkuwar abubuwan da ka iya haifar da tashin hankali a garuruwansu.

Abubakar ya ce "Ba gwamnati kadai za ta iya samar da tsaro ba. Kowa yana da rawar da zai taka wurin bayar da bayyanai masu amfani ga hukumomin tsaro. Idan ka ga bakon fuska a unguwar ku ko wadanda ke neman tayar da rikici, hakkin ka ne a matsayin dan kasa ka sanar da jami'an tsaro.

"A bangarenta, ya kamata gwamnati ta samar wa al'umma ayyukan yi da ababen more rayuwa da zai sa suyi watsi da aikata abubuwan da zai haifar da fitina."

A kan batun tsaro, Gwamna Seyi Makinde ya ce ya fara tattara bayanai kan hukumomin tsaro da nufin gano barakar da ake da su domin a dakile su.

Ya bayar da tabbacin cewa mutane za su ga canji a harkar tsaro cikin 'yan kwana kin nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel