Sabbin ministoci: Ina fuskantar matsin lamba mai tsanani - Buhari

Sabbin ministoci: Ina fuskantar matsin lamba mai tsanani - Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya magantu a kan yawaitar kiraye-kirayen da ake yi masa a kan bayar da sabbin mukamai, musamman batun nada sabbin ministoci.

Da ya ke jawabi ga shugabannin majalisar tarayya yayin cin abincin dare ranar Alhamis a Abuja, shugaban kasar ya bayyana cewa ya na fuskantar matsin lamba mai tsanani a kan nadin sabbin ministoci.

"Ina sane da dukkan abubuwan da jama'a ke fada a kan batun nadin sabbin ministoci, ni ma ina fuskantar matsin lamba a kan hakan," a cewar Buhari.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, "a baya na nada ministoci da mafi yawansu ban sansu ba. Jam'iyya ce ta bani sunayensu da shawarar na basu mukami. Haka na yi aiki tare da su na tsawon shekaru uku da rabi."

Buhari, ya bayyana cewa an samu jinkirin nada ministoci wannan karo ne saboda ya na son nada mutanen da ya san su kuma suka san shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel