Rashawa: Kotu ta aike da tsohon shugaban NIHSA gidan yari

Rashawa: Kotu ta aike da tsohon shugaban NIHSA gidan yari

Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon Direkta Janar na Hukumar da ke alhakin kula da harkokin ma'adinnan ruwa da binciken su wato Nigeria Hydrological Services Agency (NIHSA), John Shamonda hukuncin zaman gidan yari na shekara daya.

A jawabin da mai magana da yawun hukumar yaki da rashawa ta ICP,Rasheedat Okoduwa,ta fitar a ranar Alhamis, ta ce an gurfanar da Mista Shamonda a gaban Justice Adeniyi Ademola na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja kan zarginsa da aikata laifuka 10 masu alaka da karkatar da kudi har naira miliyan 603.

Hukumar ta ce laifin da Mista Shonda ya aikata ya sabawa sashi na 16, 17(1) (c) da 22 (5) na dokar masu aikata rashawa da laifuka masu alaka da rashawar.

DUBA WANNAN: Yanzunnan: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

ICPC ta kara da cewa wanda aka yanke wa laifin bai amince da dukkan laifukan da aka tuhume shi da aikatawa ba.

A yayin zaman kotun, lauya mai shigar da kara ya gabatar da shaidu bakwai da kuma takardu 26 domin tabbatar da laifin wanda ake tuhuma.

Ya kuma fadawa kotu cewa Mista Shomonda ya karbi naira miliyan 603 a shekarar 2012 domin gyaran kayyakin aiki da suka lalace a hukumarsa da yayin ambaliyar ruwa da ta faru yayin da ya ke shugaban NIHSA.

An kuma ce bai bi ka'ida ba wurin karbar kudin wadda daga baya rika kashe wa wurin sayan motocci da shirya taruruka da rabawa ma'aikata a matsayin allawus na bikin sallah.

Sai dai alkalin kotun ya ba shi zabin biyan tarar 50,000 kan laifuka 5 da suka tabbata cikin 10 da ake tuhumarsa da aikatawa duba da cewa babu kudin da aka samu zuwa asusun ajiyarsa dai dai almubazaranci da ya yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel