Osun 2022: Tsohon minista ya nemi shugaban PDP ya yi murabus kan tsayar da Adeleke takara

Osun 2022: Tsohon minista ya nemi shugaban PDP ya yi murabus kan tsayar da Adeleke takara

- Sanata Akinlabi Olasunkanmi ya fadawa shugaban PDP na jihar Osun, Soji Adagunodo da jigo a jam'iyyar Diran Odeyemi suyi murabus daga kujerunsu

- Olasunkanmi ya zargi mutanen biyu da saba dokar jam'iyyar yayin da suka bawa Sanata Adeleke tikitin takarar gwamna a 2022 ba tare da hamayya ba

- A martaninsa, Odeyemi ya ce Olasunkanmi tsohon dan siyasa ne da aka dena yayinsa wanda bai fahimci kudin tsarin mulkin jam'iyyar ba

Tsohon Ministan Cigaban Matasa kuma Jigo a Jam'iyyar Peoples Democratic party (PDP) a jihar Osun, Sanata Akinlabi Olasunkanmi, ya bukaci shugaban jam'iyyar na jihar, Soji Adagunodo da Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam'iyyar na Kasa, Diran Odeyemi suyi murabus.

Wakilin Legit.ng a Osun, Sola Adetona ya ruwaito cewa tsohon ministan ya yi wannan jawabin ne a ranar Alhamis 11 ga watan Yuli yayin da ya ke martani kan zaben Sanata Ademola Adeleke a matsayin dan takarar gwamna na jam'iyyar a 2022 ba tare da hamayya ba.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

An ruwaito cewa wasu shugabanin jam'iyyar ta PDP ne suka zabi Adeleke a matsayin dan takarar gwamnan jam'iyyar yayin taron addu'a da aka shirya a kauyen su Adeleke, Ede.

Adeleke dai ya sha kaye ne a hannun Gboboye Oyetola na jam'iyyar APC bayan an gudanar da zaben raba gardama a jihar.

Adeleke ya kallubalanci nasarar Oyetola a kotu inda daga karshe kotun koli ta tabbatarwa Oyetola na jam'iyyar APC nasararsa a kwana kwanan nan.

A yayin da ya ke mayar da martani murabus da aka nemi ya yi, Odeyemi ya ce Olasunkanmi tsohon jigo a siyasa da aka dena yayin sa.

Ya ce Olasunkanmi ya yi kuskure na neman suyi murabus saboda kawai sun hallarci taron addu'a a gidan Adeleke da ke Ede a ranar Talata 9 ga watan Yuli.

Odeyemi ya ce idan da tsohon ministan ya san gaskiyan abinda ya faru, da ya gane cewa ba shugabanin jam'iyya na jihar bane suka bukaci a tsayar da Sanata Adeleke kuma ba shugabanin jam'iyyar na jiha suka goyi bayan hakan ba, Hasali, umurnin ya zo ne daga wani shugaban jam'iyyar a matakin tarayya da ke da ikon bayyana ra'ayinsa a irin wurin taron siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel