Buhari ya gana da zababen shugaban UNGA

Buhari ya gana da zababen shugaban UNGA

A yau Alhamis, 11 ga watan Yuli Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da zababen Shugaban Majalisar Wakilai ta Dinkin Duniya (UNGA) kuma wakilin Najeriya a Majalisar, Tijjani Muhammad-Bande inda ya taya shi murna kan zabensa da a kayi a watan Yuni.

A jawabin da mai bawa shugaban kasa shawara kan kafafen yada labarai ya fitar a Abuja, Shugaba Buhari ya bukaci sabon shugaban na UN da kada ya bawa 'yan Najeriya da sauran duniya kunya bisa amanar da aka damka a hannunsa.

"Ka yi shiri sosai saboda wannan matsayin saboda irin karatun da kayi da kwarewa a fanin ka kuma haka yasa takwarorinka suka zabe ka," inji Buhari.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

"Yanzu lokaci ne da za ka yi wa wadanda suka damka maka amana sakayya."

Wannan itace ziyarar da ya kawo Najeriya tun bayan zabensa da akayi a matsayin shugaban Shugaban Majalisar Wakilai ta Dinkin Duniya a ranar 4 ga watan Yunin 2019 a birnin New York.

A jawabin da ya yi, Muhammad-Bande ya yi alkawarin cewa zai mayar da hankali wurin magance matsalolin da ke adabar Najeriya da suka hada da samar da zaman lafiya da tsaro, rage talauci, ilimi, dumamar yanayi musamman a Tafkin Chadi.

Ya kuma shaidawa manema labarai na gidan gwamnati cewa yaki da rashawa da dawo da kudaden Najeriya da ke kasashen ketare suna daga cikin abubuwan da zai bawa muhimmanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel