Da zafi-zafi: Shugaba Buhari na cikin ganawa da shugabannin majalisar dokokin kasar

Da zafi-zafi: Shugaba Buhari na cikin ganawa da shugabannin majalisar dokokin kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli ya yi ganawar sirrin da Shugabanin majalisar dokokin kasar.

Shugaban majalisar dokokin kasar kuma Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya jagorancin kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran shugabannin zuwa liyafar cin abincin dare tare da Shugaban kasar.

An fara liyafar cin abincin ne da misalin karfe 8:30 na dare a dakin taro na fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Sanata Abdullahi Yahaya, Shugaban masu rinjaye a majalisa, Sanata Ajayi Borofice, mataimakin Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, bulaliyar majalisar dattawa da kuma Sanata Sabi Abdullahi, mataimakin bulaliyar majalisar dattawa.

Sauran sun hada da Emmanuel Bwacha, Philip Aduda, bulaliyar marasa rinjaye a majalisa, Alhassan Ado-Doguwa, Ndudi Godwin Elumelu, Toby Okechukwu.

Har ila yau sauran da suka halarci taron harda babban mai ba Shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisar dokoki, Ita Enang.

KU KARANTA KUMA: Yan majalisa na APC sun yi kira ga tsige Gwamna Obaseki

Ana sanya ran cewa shugabannin majalisar dokokin za su iya samun jerin sunayen ministocin majalisar zartarwa na gaba a taron.

Har yanzu dai ana kan taron a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel