AFCON 2019: Dangote da Otedola sun yi wa Super Eagles wani babban albishir

AFCON 2019: Dangote da Otedola sun yi wa Super Eagles wani babban albishir

Attajiran 'yan kasuwa a Najeriya Aliko Dangote da Femi Otedola sun yi wa tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles alkawarin zunzurutun kudi dalla 75,000 a duk lokacin da suka zirra kwallo a ragar abokan karawarsu a sauran wasannin da za su buga a gasar cin kofin Afirka (AFCON).

Dangote ya yi alkawarin bayar da dalla 50,000 yayin da Otedola ya yi alkawarin bayar da dalla 25,000 a duk lokacin da Super Eagles ta zirra kwallo.

A farkon gasar ta AFCON 2019, Aiteo Group daya daga cikin kamfanin da ke daukan nauyin Super Eagles ta bawa tawagar kyautan dalla 75,000 saboda kwallaye uku da suka zirra a ragar Kamaru a wasar da su kayi nasara aka tashi 3 - 2.

DUBA WANNAN: An kama wasu mata 4 dumu-dumu suna madigo a Kwallejin Kimiyya a Kebbi

Dan kasuwa, Hosea Wells Okunbo ya yi alkawarin bawa kowanne dan wasan tawagar ta Najeriya dalla 20,000 yayin da gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi alkawarin bawa kowanne dan wasa dalla 5,000.

Super Eagles sun yi nasarar doke Bafana-Bafana na kasar Afirka Ta Kudu inda tashi wasar 2-1 wadda hakan ya bawa Najeriya damar zuwa matakin kusa da na karashe da za a buga a daren Laraba a filin motsa jiki na Cairo.

Super Eagles za ta buga wasan ta da wanda ya yi nasara tsakanin Alegria da Cote D'Ivoire a wasar na kusa da na karshe.

A baya bayan nan ne Femi Otedola ya bawa tsohon cocin Najeriya Christian Chukwu tallafin dalla 50,000 sakamakon rashin lafiya da ya ke fama da ita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel