Sauraron karar zaben 2019 ya hada Magoya bayan Buhari da Atiku

Sauraron karar zaben 2019 ya hada Magoya bayan Buhari da Atiku

An samu wasu kungiyoyin da ke goyon bayan manyan ‘yan takarar shugaban kasa a babban zaben 2019 watau Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar, da ke maidawa juna kalamai a halin yanzu.

Daily Trust ta rahoto mana cewa kungiyar Buhari Media Organization (BMO) mai rajin kare shugaban kasa Buhari ta yi Allah-wadai da wakilcin da PDP ta tura Farfesa Ben Nwabueze a kotu.

Kungiyar ta nuna cewa neman suna ne ya jawo Ben Nwabueze ya wakilci ‘dan takarar PDP na shugaban kasa a wajen zaman shari’ar da a ke yi tsakanin Buhari da shi Alhaji Atiku Abubakar.

BMO ta fitar da wannan jawabi ne ta bakin shugabanta da kuma babban Sakatarenta na kasa; Niyi Akinsiju da Cassidy Madueke. Shugabannin na BMO sun yi wannan jawabi ne a makon nan.

KU KARANTA: Mun ba kotu hujjar da ke nuna Buhari bai ci zabe ba - Buba Galadima

A Ranar Talata 9 ga Watan Yuni, Niyi Akinsiju ya ce Atiku Abubakar ya riga ya sha kashi a zaben 2019, don haka ta nemi ya daina wasu wala-wala da nufin nunawa Duniya cewa ba haka ba.

Tuni kungiyar Justice Vanguard wanda ke tare da tafiyar Atiku, ta yi maza ta maidawa BMO raddi inda ta ce an fara tona asirin APC. Shugaban wannan kungiya Ezekiel Adeojo ya fadi haka.

A cewar Mista Ezekiel Adeojo, irin shaidu da tarin hujjojin da PDP ta gabatar a gaban kotun da ke sauraron karar zaben na 2019, ya fara tadawa Magoya bayan shugaban kasa Buhari hankali.

Adeoju ya fitar da jawabi ya na cewa abin da Lauyoyin Atiku Abubakar su ke gabatarwa a gaban kuliya ya tabbatar da cewa babu shakka APC ta tafkawa PDP magudi ne a zaben shugaban kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel