Yan majalisa na APC sun yi kira ga tsige Gwamna Obaseki

Yan majalisa na APC sun yi kira ga tsige Gwamna Obaseki

Mambobin majalisar dokokin jihar Edo karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), sun yi kira ga a yi gaggawan tsige gwamnan jihar, Mista Godwin Obaseki.

Kiran na zuwa ne akan ikirarinsu na cewa Gwamnan ya hana a rantsar da zababbun mambobin majalisar dokokin jihar.

Kungiyar a wani jawabi daga Edoror Sabor, Saed Oshiomole, Ojiezele Sunday, Vincent Uwadiae, Osifo Washington, Sunday Aghedo, Okaeben Christopher, Crosby Eribo da kuma Okunbor Nosayaba, sun yanke shawarar cewa majalisar bata yi amanna da gwamnatin Godwin Obaseki ba wajen aiwatar da ayyukansa a ofishinsa don haka sun nemi ayi gaggawan tsige gwamnan.

Sun bayyana cewa "ya gaza mussamman a bangarorin tsaro, samar da ayyuka da kuma ci gaban kakkara.

"Samar da hukumomin jihar ba tare da sani da amincewar majalisar dokokin ba, da dai sauransu".

KU KARANTA KUMA: Zanga-zanga: An kashe dan Shi'a daya a Kaduna

A wani labarin kuma Legit.ng ta rahoto cewa, Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, a ranar Alhamis ta ki amincewa da nadin Aliyu Ja'afaru a matsayin kwamishina saboda wani rubutu da ya taba wallafawa a Facebook inda ya ke aibanta tsare-tsaren Ilimi na gwamnatin Nasir El-Rufai.

El-Rufai ya zabi Mista Jafaru mai shekaru 42 a matsayin kwamishinan Ayyukan Noma.

Baya ga Jafaru wanda malami ne a Jami'ar Jihar Kaduna, Majalisar ta tantance dukkan sauran wadanda aka yi wa naddin tare da tabbatar da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel