Abin da wasan Super Eagles da Kasar Afrika ta Kudu ya nuna

Abin da wasan Super Eagles da Kasar Afrika ta Kudu ya nuna

A Ranar Larabar nan ne da dare Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi nasarar doke kasar Afrika ta Kudu da ci 2-1 a gasar cin Nahiyar kofin Afrika watau AFCON da a ke bugawa a kasar Masar.

Mun tsakuro wasu daga cikin abubuwan da jama’a su ka fahimta daga wannan wasa:

1. Chukweze babban tauraro ne

Duk wanda ya kalli wasan Super Eagles zai fahimci cewa lallai ‘Dan kwallon nan Samuel Chukwueze ya kai ‘dan kwallo inda ya ci wa Najeriya kwallo, kuma ya rika ratsa bayan ‘Yan adawa.

2. Rauni a gaban Najeriya

Ya kamata ‘yan wasan gaban Najeriya su samu kyakkyawar fahimta da juna muddin a na neman nasara. A dalilin wannan rashin fahimta ne ‘yan wasa irin su Ahmed Musa da Ighalo su ke barar da kwallaye.

KU KARANTA: Gasar AFCON: Zafin ci ya sa Masar ta sallami Kocin ta

3. Akwai kallo a gaba

Alamu na nuna cewa za a doka wasa mai zafi idan Najeriya ta hadu da kasar hamayya ta gaba watau Aljariya. Za a yi kallo a wannan wasa, kuma babu mai iya cewa komai har sai an tike an tashi.

4. Fasaha ta na aiki

A wasan jiya, Duniya ta ga ranar fasahar zamani bayan an samu tababa a game da kwallon da a ka ci Najeriya. Na’urorin VAR sun bi sun nuna cewa halataciyya kwallo ‘Dan wasa Zuntu ya zurawa Najeriya.

5. Koyawa Afrika ta Kudu darasi

Super Eagles sun nunawa kasar Masar yadda a ke doke Afrika ta Kudu. Najeriya ta nuna kwarewa a wannan wasa ta hanyar lallasa kasar adawar tare da kuma hana ta kai harin mamayar da ta saba kai wa a baya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel