Zanga-zanga: An kashe dan Shi'a daya a Kaduna

Zanga-zanga: An kashe dan Shi'a daya a Kaduna

Rahoto da ke zuwa mana ya nuna cewa an sake samun salwantar rai a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli yayin zanga-zangar mabiya kungiyar shi’a da ke neman a saki shugabansu, Malam El-Zakzaky a jihar Kaduna.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa mabiya kungiyar sun tabbatar da cewar an kashe masu mutum daya mai suna Ahmad a wajen zanga-zangar da suka gudanar a yau Alhamis.

An kuma tattaro cewa da mutane dama daga cikin yan shi’ar sun samu raunuka a yayin gangamin.

Yan Shi’an sun gudanar da zanga zangar ne don nuna bacin ransu da cigaba da rike jagoransu Malam Ibrahim Zakzaky da gwamnatin Najeriya ta kama tun shekaru 4 da suka gabata.

A wani lamari makamancin haka mun ji cewa Mambobin Kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da akafi sani da Shi'a sun sake arangama da jami'an 'Yan sanda a Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja a yau Alhamis 11 ga watan Yuli.

KU KARANTA KUMA: Da dumi dumi: Yan Shia suna gudanar da zanga zanga a garin Kaduna

'Yan sandan sun rika harbe bindiga da borkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar yayin da aka kama mutane biyar cikin masu zanga-zangar.

The Punch ta ruwaito cewa arangamar ya haifar da tashin hankali inda ma'aikata da masu ababen hawa suka rika tserewa domin kada rikicin ya ritsa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel