Yanzunnan: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

Yanzunnan: Jonathan ya roki wata alfarma ta musamman a wurin gwamnatin Buhari

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, a ranar Alhamis 11 ga watan July ya bukaci a aiwatar da shawarwarin da aka bayar yayin taron kasa da akayi a 2014.

Jonathan ya yi wannan jawabin ne a wurin taron kaddamar da wata littafi da aka wallafa don bikin cika shekaru 80 na goggagen dan siyasa, Sanata Okurounmu.

Kamfanin Dilllancin Labarai na Kasa (NAN) ta ruwaito cewa Jonathan ya ce ya kira taron kasar ne a zamanin mulkinsa domin gano hanyoyin magance wasu matsaloli da kasar ke fuskanta a lokacin.

A cewarsa, wasu daga cikin matsalolin da ke adabar kasar musamman kan tsaro da hadin kan kasa suna nan suna cigaba da haddasa fitina a kasar.

DUBA WANNAN: An kama wasu mata 4 dumu-dumu suna madigo a Kwallejin Kimiyya a Kebbi

Jonathan ya ce, "Na san cewa ana daukan wasu matakai domin magance wasu daga cikin matsalolin amma kamar muna jefa siyasa cikin abubuwa masu muhimmanci.

"Mutane na cigaba da neman ganin anyi canje-canje kan yadda ake tafiyar da mulki a kasar kuma ya zama dole a saurare su idan har ana son ganin cigaba a kasar.

"Nayi imanin cewa za mu samu hanyoyin wareware matsalolin da muke fama da su a yau idan aka aiwatar da shawarwarin da aka bayar yayin taron kasa na 2014.

"Idan muka dena jefa siyasa cikin lamaran kasar nan, akwai yiwuwar kaddamar da shawarwarin da kwamitin taron kasar ta bayar za su warware matsalolin kasar".

Tsohon shugaban kasar ya ce bai samu ikon kaddamar da shawarwarin bane a zamanin mulkinsa saboda daf da zabe ne aka mika masa shawarwarin kuma a lokacin 'yan majalisa sun mayar da hankali ne kan zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel