Jerin sunayen sabbin hadiman Kakakin Majalisar wakilai su 6

Jerin sunayen sabbin hadiman Kakakin Majalisar wakilai su 6

-Kakakin Majalisar wakilai ya nada sabbin hadimai guda shida wadanda zasu kula ma shi da sashen labarai

-Femi Gbajabiamila da kansa ne ya bada wannan sanarwar a ranar Alhamis inda ya bayyana sunan hadiman nasa guda shida

Kakakin Majalisar Wakilai, Hon Femi Gbajabiamila ya nada hadimansa wadanda zasu taimaka masa a kan yada labarai.

A wani zance da ya samu sanya hannun Kakakin da kansa, ya ce: “ Ina mai matuqar farin cikin sanar da al’ummar Najeriya nadin sabbin hadiman da zasu kula min da sashen yada labarai.”

KU KARANTA:Zaben Kogi: APC ta za ta dubi korafin masu bore a kan zaben fidda dan takarar Gwamna

Ga sunayen hadiman kamar haka:

Olanrewaju Lasisi – A matsayin mai bada shawara na musamman kan lamuran yada labarai

Kafin nadin Olanrewaju Lasisi, mai shekaru 46, ya kasance wakilin tashar Channels Tv wanda ke kawo masu rahoton Majalisar wakilai. Yana da kwarewa a kan aikin jarida sosai domin ya kwashi kimanin shekaru 10 yana aikin. Haka zalika shi ne ke gabatar da shirin “ The Gavel” wanda ke dauko bayanai a kan Majalisar dokokin Najeriya.

Musa Abdullahi Krishi – A matsayin sakataren yada labarai

Har zuwa lokacin da aka nada Musa Abdullahi Krishi mai shekaru 33 da haihuwa ya kasance ma’akacin jaridar Daily Trust inda yake dauko rahoto daga Majalisar dokoki. Ya samu tsawon shekaru 6 yana kawo rahotanni daga Majalisar wakilai.

Bukola Ogunyemi – Maitamakawa Kakakin a fannin sabuwar hanyar sadarwa

Bukola Ogunyemi mai shekaru 32, ya kasance kwararre wajen amfani da hanyoyin sadarwa na sada zumunta inda har yake aiki da wani kamfanin kasar Amurka mai suna World WildLife Fund dake birnin Washington DC.

Dele Anofi – Mataimakawa wurin fitar da sakonni a rubuce

Dele Anofi mai shekaru 52, ya kasance wakilin jaridar The Nation a Majalisar wakilai na tsawon shekaru bakwai (7).

Kunle Somoye – Mataimakawa kan hanyoyin sadarwar zamani

Kunle Somoye mai shekaru 26, kwararre ne a fannin bincike mai zurfi da ya shafi ayyukan sadarwa.

Ayo Adeagbo – Mai daukan kakakin hoto na musamman

Ayo Adeagbo mai shekaru 25, kafin nada shi wannan muqamin, shi ne tsohon mai daukan hoto a Majalisar jihar Oyo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel