Yanzu-yanzu: An cimma yarjejeniya tsakanin manyan makarantun kasar waje da Engr. Rabiu Musa Kwankwaso

Yanzu-yanzu: An cimma yarjejeniya tsakanin manyan makarantun kasar waje da Engr. Rabiu Musa Kwankwaso

- Bayan tafiyar tsohon sanatan Kanon, rahotanni sun nuna cewa akwai alamun nasara a tafiyar tashi

- Inda a yanzu haka rahotanni suka bayyana cewa tsohon gwamnan ya cimma matsaya tsakaninsa da manyan makarantun jami'a na kasar ta Indiya

- Kwankwasi yana wannan hubbasa ne domin ganin ya cika alkawuran da ya dauka na ganin ya kai 'ya'yan talakawa karatu kasar ta Indiya kamar yadda ya sha alwashi

A rahoton da muke samu ya nuna cewa an cimma matsaya tsakanin manyan makarantun jami'a na kasar Indiya da Engr. Rabiu Musa Kwankwaso.

Kwankwaso ya kai ziyara kasar Indiyan ne domin nemawa dalibai 370 guraben karatun digiri na biyu a kasar, wanda gidauniyar Kwankwasiyya Development Foundation ta dauki nauyi karkashin jagorancin tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Engr. Rabiu Musa Kwankwaso.

KU KARANTA: Kudi masu gidan rana: Hotunan bikin Fatima Abdulkadir Abacha kenan 'ya gurin dan uwan Marigayi Sani Abacha

Yanzu haka dai komai ya kankama tsakaninsa da makarantun jami'ar kasar ta Indiya.

A cikin wannan makon ne tsohon gwamnan Kanon, kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya ya kai ziyara kasar ta Indiya domin nemawa daliban da yayi alkawarin daukar nauyin karatunsu gurbin karatun digiri na biyu a kasar ta Indiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel