To fah: Cin mutuncin Naira babban ta'addanci ne - Babban Banki

To fah: Cin mutuncin Naira babban ta'addanci ne - Babban Banki

Babban bankin Najeriya (CBN), ta roki yan Najeriya da su daina bata sifar naira, inda ta bayyana kudin a matsayin shaidar kasar, wanda ya zama dole a barta cikin tsafta a koda yaushe.

Dr Isaac Okorafor, daraktan bangaren sadarwa na CBN, ya yi wannan rokon a wani shiri mai taken “CBN Fair” a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli a Osogbo.

Okorafo yace yadda mutane ke muzanta naira ya kasance abun damuwa ga babbar bankin kasar.

Da ya samu wakilcin Mista Samuel Okogbue, wani mataimakin Darakta a kamfanin, Okorafor yace naira alama ce ta hadin kan kasa wanda ya zama dole a mutunta.

Okorafor ya roki yan Najeriya da su dunga mutunta naira sosai sannan su dunga yi masa riko na musamman cikin tsafta.

“Bamu da wai kudi baya ga naira kuma ya zama dole mu mutunta shi.

“Naira ce alamar mu da kuma mutuncinmu a matsayin kasa don haka ya zama dole mu yi masa riko na musamman.

“Kada ku lika sa, ko yin rubutu a kai maimakon haka ku mutunta shi. Cin mutuncin naira babban laifi ne wanda ke tattare da hukunci.

KU KARANTA KUMA: Ta faru ta kare: A gabana aka dinga canja sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 - Yahaya Shiko

“Kamar yadda muke mutunta tutar kasarmu, mu mutunta naira ma.

“Abun bakin ciki e yadda mutane ke cin mutuncin naira ta hanyar rubutu a kai, da lika sa," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel