Ku yi watsi da zancen: NNPC ta karyata labarin karin kudin farashin mai

Ku yi watsi da zancen: NNPC ta karyata labarin karin kudin farashin mai

Kamfanin dillan man fetur na kasa (NNPC) ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi watsi da zancen da ke yawo a gari a kan cewa za a kara farashin man fetur.

A wani takaitaccen sako da NNPC ta fitar a shafinta na Tuwita ta karyata batun cewa sabon shugabanta, Mele Kyari, ya ce za a kara farashin man fetur.

Jaridu da dama da suka hada da Legit.ng sun rawaito cewa Mele Kyari, sabon shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPC, ya ce abu ne mai matukar wahala a ci gaba da samar da man fetur cikin kasar nan a kan farashin naira 145 na kowace ita guda.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, sabon shugaban na NNPC ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, a ofishin sa na majalisar tarayya dake babban birnin Tarayya.

A cewar sa, rahusa da farashin man fetur ke da ita a halin yanzu na da tasiri wajen angiza badakalar shigo da haramtattun kayayyaki da 'yan sumoga ke yi a kasar nan.

DUBA WANNAN: Karar kwana: Yadda mutane biyu suka mutu yayin gyaran fitilar haskaka titi a Kaduna

Ya kara da cewa, saukin farashin naira 145 na kowace lita guda ta man fetur a kasar nan sabanin yadda ake sayar da shi a kan naira 350 cikin sauran kasashen yankin Afirka ta Yamma na taka rawar gani wajen bayar da gudunmuwar sumoga a Najeriya.

Kazalika ya ce, abu ne mai matukar wahala da babu lallai a iya ci gaba da samar da man fetur a kan naira 145.

Sai dai NNPC ta karya wannan batu, ba ta bayar da wani karin haske a kan musabbabin yada jita-jitar cewa za a kara farashin na man fetur ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel