Buhari ya nemi amincewar majalisar dattawa a kan sake nadin wasu hadiman sa 15

Buhari ya nemi amincewar majalisar dattawa a kan sake nadin wasu hadiman sa 15

Shugaban kasa Muhamadu Buhari, ya sake aikewa da wata wasika zuwa majalisar dattawa ta Najeriya, inda yake neman sahalewarta a kan nadin wasu sabbin hadimansa 15 a yayin da kundin tsarin mulkin kasa ya bashi dama.

Wannan ita ce wasika ta biyu da shugaban kasa Buhari ya aike da ita zuwa majalisar tarayyar kasar nan a yau Alhamis 11 ga watan Yulin 2019. Buhari a baya ya aike da wasikar neman amincewar majalisar dattawa a kan tabbatar da nadin mukamin alkalin alkalai, Justice Tanko Muhammad.

A wasikar sa ta biyu duba da tanadin sashe na 151 cikin kundin tsarin mulkin kasar nan, shugaban kasa Buhari ya nemi amincewar majalisar dattawa a kan nadin wasu hadimai 15 da za su taya sa wajen sauke nauyin al'ummar kasar nan da rataya a wuyan sa.

Cikin karamci gami da dattako na neman alfarma, shugaba Buhari ya aike da rubutacciyar wasikar sa zuwa majalisar dattawa domin neman sahalewarta a akan tabbatar da nadin hadiman sa na musamman da yayi ikirarin kyautata zato na samun biyan bukatar dattawan kasar nan.

KARANTA KUMA: Mai daki na sai ta bukaci cin hanci kafin na tara da ita - Aboyomi

A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, gwamnatin shugaban kasa Buhari ta tara fiye da naira tiriliyan 10 ta hanyar tsarin asusun bai-daya na TSA da ta tabbatar tun a watan Agustan 2015, bayan karbar ragamar jagoranci a hannun tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel