Karar kwana: Yadda fitilar haskaka titi ta kashe mutum biyu a Kaduna

Karar kwana: Yadda fitilar haskaka titi ta kashe mutum biyu a Kaduna

Wasu mutane biyu da majiyar mu ba ta san sunayensu ba sun mutu sakamakon jan su da wutar lantarki ta yi yayin da suke gyaran fitilar haskaka titin NNPC a garin Kaduna.

Majiyar mu ta sanar da mu cewa mutanen biyu sun gamu da ajalinsu bayan sun yi amfani da tsani na karfe domin gyaran fitilar.

Mutanen biyu; wanda ya hau tsanin da wanda ya rike, duk sun mutu sakamakon jan su da wutar lantarki ta yi.

Wasu shaidar gani da ido sun bayyana cewa wata babbar wayar wutar lantarki ce ta fado a kan tsanin karfen a daidai lokacin da suke tsaka da gyaran fitilar titin.

Lamarin ya faru ne ranar Talata, 9 ga watan Yuli.

Sai dai, majiyar mu ta bayyana cewa ba ta da masaniyar inda aka ajiye gawar mutane bayan an kwashe su.

A daren ranar Laraba ne jaridar Legit.ng ta wallafa wani rahoto a kan yadda hukumomin asibitin Yusuf Dantsoho da ke Tudun Wada a garin Kaduna suka bayyana damuwarsu a kan yawaita jibge gawar mutane da jami'an 'yan sanda ke yi a dakinsu na ajiye gawa ba tare da gabatar da kowacce irin takarda ba.

A wani bincike da Arewa Trust da ke fita duk karshen mako ta gudanar ya nuna cewa a cikin shekara guda jami'an 'yan sanda sun kai ajiyar gawa guda takwas asibitin ba kuma tare da sun kara waiwayarsu ba.

KARANTA CIKAKKEN RAHOTON: Wani asibiti a Kaduna ya koka bisa yadda 'yan sanda ke yawan kai ajiyar gawar mutane

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel