Ta faru ta kare: A gabana aka dinga canja sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 - Yahaya Shiko

Ta faru ta kare: A gabana aka dinga canja sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 - Yahaya Shiko

Wani jami’in jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a lokacin zaben Shugaban kasa na 2019, Yahaya Shiko, ya yi zargin cewa a Kaduna, an canja sakamakon zaben ne don ganin Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi nasara.

Shiko, wanda yayi aiki a matsayin jami;’in tattara sakamako na PDP a karamar hukumar Kaduna ta kudu da ke jihar Kaduna, yayi ikirarin ne a kotun zabe a ranar Alhamis, 11 ga watan Yuli.

Yace an canja dukkanin sakamakon ne a gabansa.

Jam’iyyar PDP da dan takararta na Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar na kalubalantar sakamakon zaben wanda ya bayyana Shugaban kasa Buhari a matsayin wanda yayi nasara.

Da yake jawabi a matsayin saida na 20, Shiko yace zaben da aka gudanar a yankin shi cike yake da zarcewar kuri’u da kuma rarrabawa jam’iyyu adadin kuri’u.

KU KARANTA KUMA: Likafa ta ci gaba: Yan shi’a sun yi zanga zanga a Lagas, sun bukaci a saki El-Zakzaky

A bangare daya, mun ji cewa wani wakilin jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2019 ya bayyana wa kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) ta hada baki da jam'iyyar APC wajen kara yawan mazabu fiye da 1,000 a jihar Borno.

Shaidar, Nickolas Shediza, wakilin jam'iyyar PDP na jiha, ya shaida wa kotun cewa yana da masaniyar cewa jihar Borno na da jimillar mazabun zabe 3,933 amma sai hukumar zabe ta kara yawansu zuwa 5078 yayin zabukan shekarar 2019.

Shediza ya yi zargin cewa adadin kuri'u 919,786 da INEC ta sanar an kada a jihar Borno yayin zaben shugaban kasa sun haura adadin yawan mutanen da INEC ta sanar cewa an tantance yayin zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel