Zaben Kogi: APC ta za ta dubi korafin masu bore a kan zaben fidda dan takarar Gwamna

Zaben Kogi: APC ta za ta dubi korafin masu bore a kan zaben fidda dan takarar Gwamna

-APC za ta duba korafin masu takarar gwamnan Kogi kan batun zaben fidda gwani

-Kakakin jam'iyyar na kasa Lanre Issa-Onilu ne ya fadi wannan magana jiya Laraba a sakatariyar jam'iyyar APC da ke Abuja

-Mutum 20 ne daga cikin 'yan takarar suka nuna rashin amincewarsu da yin zaben na fidda gwani a asirce

Kwamitin zartarwa na APC a matakin kasa, ya bada tabbacin cewa zai duba korafin da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC a Kogi suka yi, na nuna bacin ransu bisa cewa za’a gudanar da zaben fidda gwani a asirce domin zabar wanda zai wakilici APC a zaben gwamnan jihar dake tafe a ranar 16 ga Nuwamba.

Kakakin jam’iyyar na kasa, Malam Lanre Issa-Onilu ne ya fadi a wani zancen da ya fitar jiya Laraba a Abuja, “ Kwamitin zartarwa zai duba korafin domin ganin ko ya dace da kundin tsarin dokokin jam’iyyar sa’annan mu fito da mafita.” A cewar kakakin.

KU KARANTA:Magudin jarabawa: Kwalejin Ibadan ta bankawa wayoyin salula na miliyoyin kudi wuta wanda ta karbe daga hannun dalibai

Har ila yau, Issa-Onilu, ya sake jinjinama jiga-jigan APC a jihar Kogin, a dalilin yin abinsu a tsanake ba tare da kawo wata fitina ba.

Bugu da kari, Kakakin ya sake bayyana mana cewa, kundin tsarin dokokin jam’iyyar APC hanya uku ya fadi ta gudanar da zaben fidda gwani, ko dai a asirce, ko yar tinke ko kuma hanyar tattaunawa tsakanin yan takara.

Kimanin mutum 20 ne daga cikin masu takarar gwamnan a karkashin jam’iyyar APC suka nuna rashin amincewarsu da yin zaben fidda gwani a asirce.

Daya daga cikin ‘yan takaran kuma kakakin kungiyar masu takarar gwamnan karkashin APC, Muhammad Ali ne ya karanta wasikar da kungiyarsu ta rubuta zuwa ga Shugaban APC na kasa, inda a ciki suka fadi cewa babu wanda ya tuntubesu kafin a zartar da maganar zaben fidda gwani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel