Kotu: Yadda INEC ta kara yawan mazabu fiye da dubu daya a jhar Borno - Shaidar Atiku

Kotu: Yadda INEC ta kara yawan mazabu fiye da dubu daya a jhar Borno - Shaidar Atiku

- Nickolas Shediza, wakilin jam'iyyar PDP a jihar Borno yayin zaben shugaban kasa, ya zargi INEC da hada baki da APC wajen tafka magudi

- Shaidar ya shaida wa kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa cewa INEC ta hada baki da APC wajen kara yawan mazabu fiye da 1,000 a fadin jihar Borno

- Shediza ya yi zargin cewa adadin kuri'u 919,786 da INEC ta sanar an kada a jihar Borno yayin zaben shugaban kasa sun haura adadin yawan mutanen da INEC ta sanar cewa an tantance yayin zaben

Wani wakilin jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2019 ya bayyana wa kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa yadda hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) ta hada baki da jam'iyyar APC wajen kara yawan mazabu fiye da 1,000 a jihar Borno.

Shaidar, Nickolas Shediza, wakilin jam'iyyar PDP na jiha, ya shaida wa kotun cewa yana da masaniyar cewa jihar Borno na da jimillar mazabun zabe 3,933 amma sai hukumar zabe ta kara yawansu zuwa 5078 yayin zabukan shekarar 2019.

Shediza ya yi zargin cewa adadin kuri'u 919,786 da INEC ta sanar an kada a jihar Borno yayin zaben shugaban kasa sun haura adadin yawan mutanen da INEC ta sanar cewa an tantance yayin zaben.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai wa jami'in 'yan sanda na rundunar 'Puff Adder' harin kwanton bauna a Katsina

Sai dai, shaidar ya gaza bayyana adadin mutanen da INEC ta sanar cewa an tantance domin kada kuri'a yayin zaben shugaban kasa.

A wani rahoto da jaridar This Day ta wallafa a watan Fabrairu, ta bayyana cewa kwamishinan zabe na hukumar INEC a jihar Borno, Mohammed Magaji, ya bayyana cewa akwai adadin mazabu 3,933 da INEC ta san da zamansu a fadin kananan hukumomi 27 da ke jihar Borno.

Jaridar, har ila yau, ta kara da cewa akwai kimanin mutane fiye da miliyan 2.3 da suka yanki rijistar kada kuri'a a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel