Ganduje ya nada tsohon dan majalisa da ya kashe maganar Gandolla a matsayin shugaban KAROTA

Ganduje ya nada tsohon dan majalisa da ya kashe maganar Gandolla a matsayin shugaban KAROTA

-Gwamnan jihar Kano ya nada Baffa Babba Dan-Agundi a matsayin saban shugaban KAROTA

-Babba Dan-Agundi shine tsohon dan majalisa dake wakiltar kwaryar garin Kano a majalisar dokoki ta jihar.

-Gwamna Ganduje ya kuma sake nada Idris Wada a matsayin shugaban hukumar kula da titunan Kano (KARMA)

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nada Baffa Babba Dan-Agundi a matsayin saban shugaban hukumar kula da sufuri ta Kano (KAROTA).

Babba Dan-Agundi shi ne tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar Kano da ta shude. Ya sha kaye a zaben da ya gabata na 2019.

A cikin watan Oktoba na shekarar 2018, Babba Dan-Agundi ya jagoranci kwamitin da ya fara bincike akan wani bidiyo da aka ga gwamna Ganduje na karbar cin hanci daga wajen yan kwangila, amma suka daina binciken bayan da aka bayar da wani umurnin kotu dake da alamar tambaya.

KARANTA WANNAN: Yan Shia sun ji a jikinsu yayin wata sabuwar arangama da suka yi da Yansanda a Abuja

A wani jawabi da babban sakataren sadarwa na gwamna Ganduje, Abba Anwar ya fitar a ranar Laraba 10 ga watan Yuli 2019, gwamna Ganduje ya kuma sake nada Idris Wada a matsayin shugaban hukumar kula da titunan Kano (KARMA).

Babba Dan-Agundi shine tsohon dan majalisa dake wakiltar kwaryar garin Kano a majalisar dokoki ta jihar.

Abba Anwar ya bayyana cewa gwamna Ganduje ya yi kira ga sababbin shuwagabannin da su yi aiki tukuru saboda an zabe su ne sakamakon irin gudunmuwar da suka bayar wajen ci gaban jihar a baya.

Ya karfafa cewa “Ina fatan za ku inganta wadannan hukumomin, ku gyara su ta yadda za su yi aiki da kyau.

“Mukamin da kuka samu ya tabbatar da irin gudunmuwar da kuka bayar ga jihar. Hakan ya nuna cewa za ku bayar da karfinku wajen ganin kun inganta hukumomin da za ku jagoranta.” kamar yadda jawabin ya bayyana.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel