Aisha Buhari ta nemi babban sufeton 'yan sanda da ya magance annobar fyade a Najeriya

Aisha Buhari ta nemi babban sufeton 'yan sanda da ya magance annobar fyade a Najeriya

Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta jaddada muhimmancin tunkarar annobar fyade a Najeriya domin magance ta cikin gaggawa. Ta yi kira na neman hadin kan dukkanin masu ruwa da tsaki.

Uwargidan shugaban kasar ta yiwa wannan kira cikin wani sako da rubuta a shafin ta na zauren sada zumunta a ranar Laraba 10 ga watan Yulin 2019. Hajiya Aisha ta nemi tsayuwar dakan dukkanin masu ruwa da tsaki musamman hukumar 'yan sanda wajen magance ta'adar fyade.

Ta yi kira na neman babban sufeto 'yan sanda, Muhammadu Adamu, da kuma dukkanin masu ruwa da tsaki a kan tabbatar da shimfidar tsauraran matakai da kuma hukunci a kan masu aikata ta'adar fyade musamman ga kananan yara.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, uwargidan shugaban kasa Buhari a watan Mayun 2017, ta ziyarci wasu jaririya 'yar watanni bakwai da haihuwa a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, wadda wani Matashi mai shekaru 30 a duniya Mukhtar Muhammad ya yiwa fyade.

KARANTA KUMA: Najeriya ta samu N10tr ta hanyar asusun gwamnati na bai-daya, TSA

Har ila yau, uwargidan shugaban kasa Buhari na kan akidar ganin ta'adar fyade a mafi kololuwar mataki na zalunci da keta haddin bil Adama.

A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito mai nasaba da wannan, wani saurayi mai shekaru 14 da ya shahara a kan mummunar ta'adar yiwa 'yan mata fyade, ya shiga hannun jami'an tsaro a Arewacin kasar Jamus.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel