Kwamishina: Majalisa ta ki tantance wani da El-Rufai ya zaba saboda rubutu da ya yi a Facebook

Kwamishina: Majalisa ta ki tantance wani da El-Rufai ya zaba saboda rubutu da ya yi a Facebook

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, a ranar Alhamis ta ki amincewa da nadin Aliyu Ja'afaru a matsayin kwamishina saboda wani rubutu da ya taba wallafawa a Facebook inda ya ke aibanta tsare-tsaren Ilimi na gwamnatin Nasir El-Rufai.

El-Rufai ya zabi Mista Jafaru mai shekaru 42 a matsayin kwamishinan Ayyukan Noma.

Baya ga Jafaru wanda malami ne a Jami'ar Jihar Kaduna, Majalisar ta tantance dukkan sauran wadanda aka yi wa naddin tare da tabbatar da su.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka mallaki arzikin da ya fi kasafin kudin Najeriya

Yayin zaman tantancewar da aka gudanar a yau Alhamis, Kakakin Majalisar, Aminu Shagali ya tunawa Jafaru rubutun da ya yi a Facebook inda ya soki tsare-tsaren Ilimi na gwamnan jihar.

"Ka aibanta gwamnatin da yanzu za ta dauke ka aiki a rubutun da ka wallafa a shafin ka na Facebook.

"Ka ce babu wani abin alheri cikin tsare-tsaren Ilimi na gwamnan jihar kuma shima gwamnan ka cacake shi.

"Duk da hakan, gwamnan ya zabe ka saboda cancanta. Gwamnan ya zabe ka cikin takardun karatu na mutane 10 da aka gabatar masa, Kana ganin ya dace ka yi aiki da gwamnatin da ka ce mara inganci ne?"

Jafaru ya yi kokarin kare kansa amma amsar da ya bayar ba ta gamsar da Majalisar ba wadda hakan ya sa suka yi watsi da nadin da aka yi masa baki daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel