Likafa ta ci gaba: Yan shi’a sun yi zanga zanga a Lagas, sun bukaci a saki El-Zakzaky

Likafa ta ci gaba: Yan shi’a sun yi zanga zanga a Lagas, sun bukaci a saki El-Zakzaky

- Har yanzu mabiya kungiyar shi’a na zanga-zagar a saki shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky

- Sun gudanar da zanga-zanga a jihar Lagas a yau Alhamis, 11 ga watan Yuli

- Sun nemi gwamnatin Buhari ta bi doka ta saki shugaban nasu

Mambobin kungiyar shi’a sun sake zanga-zanga a kokarinsu na ganin an saki shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky. A wannan Karon sun kai zanga-zangar nasu har jihar Lagas.

A yakin Maryland da ke jihar Lagas, an gano daruruwan yan shi’an dauke da manyan hotunan El-Zakzaky tare da kira ga a sake shi.

KU KARANTA KUMA:

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa Jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun yi fama da mabiya mazahabar Shia a yayin da suka gudanar da wani gangamin zanga zanga a babban birnin tarayya Abuja, wanda har ta kai ga sun yi amfani da barkonon tsohuwa.

Yan shia’an suna gudanar da zanga zanga ne da nufin neman gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sako musu jagoransu, Ibrahim Zakzaky tare da matarsa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dandazon yan shia’an sun yi shirin yin zaman dirshan a dandalin Eagle Square ne, toh amma sai Yansandan kwantar da tarzoma suka ci musu birki, daga bisani kuma suka gayyaci jagororin zanga zangar, Nura Marafa da Mujahid Muhammad su fito su tattauna dasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel