'Yan bindiga sun kai wa jami'in 'yan sanda na rundunar 'Puff Adder' harin kwanton bauna a Katsina

'Yan bindiga sun kai wa jami'in 'yan sanda na rundunar 'Puff Adder' harin kwanton bauna a Katsina

'Yan bindiga, a ranar Laraba, sun kai wa jami'an 'yan sanda na rundunar 'Puff Adder' harin kwanton bauna a karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.

'Yan bindigar sun kashe dan sanda daya daga cikin tawagar 'yan sandan a yayin da suke kan hanyar zuwa wani kauye da aka sanar da su cewa an kai hari.

Karin wasu 'yan sanda hudu sun samu raunuka kafin su samu damar gudu wa zuwa cikin daji.

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Katsina, Sanusi Buba, ne ya bayyana hakan yayin da yake bajakolin wasu 'yan bindiga da barayin shanu a hedikwatar 'yan sanda ta jihar Katsina.

Ya ce 'yan bindigar da yawansu ya kai kusan 300, sun kai wa 'yan sandan hari ne a kan baburan da yawansu ya wuce 200.

Ya roki mutane da su taimaka wa rundunar 'yan sanda da muhimman bayanai domin samun damar magance 'yan bindigar da sauran 'yan ta'adda da suka addabi jihar.

DUBA WANNAN: Wani asibiti a Kaduna ya koka bisa yadda 'yan sanda ke yawan kai ajiyar gawar mutane

Kwamishina Buba ya sanar da cewa jami'an 'yan sanda sun fasa wata tawagar gungun barayin shanu da 'yan fashi da masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

Ya kara da cewa mutanensa sun samu nasarar kwace wasu makamai da ababen hawa da abinci daga wurin 'yan ta'addar.

Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewa wata tawagar 'yan sanda a karkashin jagorancin DPO na ofishin rundunar da ke Batsari, ta samu nasarar tarwatsa karin wasu gungun barayin shanu, 'yan fashi da makami, da masu garkuwa da mutane da suka addabi kananan hukumomin Batsari da Safana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel