Yan Shia sun ji a jikinsu yayin wata sabuwar arangama da suka yi da Yansanda a Abuja

Yan Shia sun ji a jikinsu yayin wata sabuwar arangama da suka yi da Yansanda a Abuja

Jami’an rundunar Yansandan Najeriya sun yi fama da mabiya mazahabar Shia a yayin da suka gudanar da wani gangamin zanga zanga a babban birnin tarayya Abuja, wanda har ta kai ga sun yi amfani da barkonon tsohuwa.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito yan shia’an suna gudanar da zanga zanga ne da nufin neman gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sako musu jagoransu, Ibrahim Zakzaky tare da matarsa.

KU KARANTA: Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 15 da zai nadasu mukamin mashawarta

Majiyar Legit.ng ta ruwaito dandazon yan shia’an sun yi shirin yin zaman dirshan a dandalin Eagle Square ne, toh amma sai Yansandan kwantar da tarzoma suka ci musu birki, daga bisani kuma suka gayyaci jagororin zanga zangar, Nura Marafa da Mujahid Muhammad su fito su tattauna dasu.

Amma fitarsu keda wuya don tattaunawar sai Yansanda suka shiga marinsu tare da jibgarsu, daga nan kuma suka yi awon gaba dasu, wannan ya harzuka yan shia’an suka yi ca a kan Yansandan, inda su kuma suka harba musu barkonon tsohuwa.

Rahotanni sun bayyana da dama daga cikin yan shia’an sun jikkata, wasu kuma sun suma a wajen.

Idan za’a tuna ko a ranar Laraba sai da aka kai gwauro aka kai mari tsakanin Yansandan Najeriya da yan Shia a farfajiyar majalisar dokokin Najeriya inda yan shia’an suka kai zanga zangarsu, tare da yin kokarin kutse cikin majalisar.

Sai dai Yansanda sun taresu, wanda hakan ya janyo tashin hankali aka raunata wasu, wasu suka suma, tare da kona motoci da kuma lalata wasu motoci da suka kai guda 50, daga cikin wadanda aka raunata akwai Yansanda 4 da yan shia da dama, yayin da yan shia’an suka ce an kashe musu mutane 2.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel