Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matasa 4 yan bautan kasa a Bayelsa

Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matasa 4 yan bautan kasa a Bayelsa

Rahoton da muka samu da dumi dumi shine wasu gungun yan bindiga sun tare wata motar Bus a jahar Bayelsa, inda suka yi awon gaba da kafatanin fasinjojin motar mutum 9, inji rahoton Sahara Reporters.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin mutane 9 dake cikin motar mai lamba BWR 362 XC akwai matasa yan bautan kasa masu yi ma kasa hidima, watau NYSC, mutane 4.

KU KARANTA: Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 15 da zai nadasu mukamin mashawarta

Majiyar ta bayyana cewa lamarin ya auku ne a ranar Talata, 9 ga watan Yuli a daidai yankin Egele na jahar Bayelsa, kan hanyar da ta tashi daga Bayelsa zuwa jahar Ribas. Sai dai akwai mutane hudu da Allah Ya tseratar bayan sun samu damar tserewa ta cikin dazuka a guje.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto babu wani labarin game da ko yan bindigan sun tuntubi iyalan fasinjojin da suka yi garkuwa dasu ko kuwa a’a, ita ma hukumar NYSC bata ce uffan akan lamarin ba.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kaakakin rundunar Yansandan jahar, Nnamdi Omoni ya bayyana cewa mutane hudun da aka ce sun tsere ba tserewa suka yi ba, Yansanda ne suka kwatosu, amma ya musanta batun kasantuwar yan bautan kasa a cikin motar.

A wani labarin kuma, hukumar Yansandan jahar Adamawa ta tabbatar da sace wani babban jami’in gwamnatin jahar, Emmanuel Piridimso, da yan bindiga suka yi a ranar Laraba.

Mista Emmanuel shine babban sakataren a ma’aikatar arzikin ma’adanan kasa na jahar Adamawa, kuma yan bindigan sun daukeshi ne daga gidansa dake rukunin gidaje na Clerk a garin Jimeta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel