Babban magana: Dan shekara 25 ya yiwa tsohuwa mai shekara 70 fyade

Babban magana: Dan shekara 25 ya yiwa tsohuwa mai shekara 70 fyade

Rundunar yan sandan jihar Imo a yanzu haka tana arautar wani mutum dan shekara 25 a duniya, Chidera Nwachukwu, wanda ake zargi da yiwa tsohuwa mai shekara 70 wacce ta kasance yar’uwarsa, Imelda Nwachukwu fyade a cikin shagonta da ke Ogwa, karamar hukumar Mbaitoli da ke jihar.

Mai kare hakkin dan adam, Harrison Gwamnishu a wata hira da akayi das hi, yace lamarin ya afku ne a ranar Litinin, 8 ga watan Yuli.

“Matar ta fada mana acewa a ranar Litinin tana zaune a shagonta inda take siyar da kayan biskiti da sauran kananan abubuwa sai matashin ya zo sannan suna hirar tafiyar da yayi zuwa Owerri. Tace nan take, sai matashin ya ture ta sannan tabuga kai da katakon da take jera kaya. Tana shiga wani yanayi na dan lokaci.

"A lokacin da ta farka sai ta ga cewa anyi mata tsirara sannan ga maniyyi a duk jikinta. Sai ta nemi agaji sannan mutanen kauyen suka cece ta. Sun gan ta zindir da maniyi a duk jikinta,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Yadda ’ya’yana maza 3 suka makance suna samari – Inji wata uwa

Emefiena yace a take mutanen kauyen suka kai ta asibiti don samun kulawar likita. A asibitin ne aka sanar masa da lamarin. Yanzu an kai rahoton lamarin zuwa ga ofishin yan sandan Ogwa sannan kuma ana kokarin kamo mai laifin da ya tsere.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel