Najeriya ta samu N10tr ta hanyar asusun gwamnati na bai-daya, TSA

Najeriya ta samu N10tr ta hanyar asusun gwamnati na bai-daya, TSA

Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta ce ta samu ikon tarawa kasa fiye da naira tiriliyan 10 ya hanyar shimfidar tsarin nan na asusun bai-daya na TSA daga ma'aikatu 1,674.

Ofishin babban Akantan Kasar, Ahmed Idris, shi ne ya bayar da shaidar hakan a ranar Alhamis 11, ga watan Yulin 2019. Ofishin ya yi wannan karin haske yayin taron nazari a kan tsar-tsaren ma'aikatu da cibiyoyin gwamnatin kasa na shekarar 2019 da aka gudanar a garin Abuja.

A yayin taron da aka gabatar a gaban shugaban ma'aikatan gwamnatin Tarayya, Misis Winifred Oyo-Ita, babban ofishin mai kula da harkokin shige da ficen kudaden gwamnatin Tarayya ya bayyana yadda asusun bai-daya ya taimaka wajen tanadin fiye da Naira biliyan 45 na kudaden ruwa a kowane wata.

Gwamnatin Najeriya na ci gaba da tara wannan kudade ta hanyar karbar kudin ruwa gabanin tabbatar da cikar tsarin asusun bai-daya a kasar nan.

Kazalika ofishin Akantan na kasa ya ribaci tsarin asusun-bai daya na TSA wato Treasury Single Account wajen karbar kudaden shiga na kimanin naira biliyan 50 daga hannun bankunan kasar nan.

KARANTA KUMA: Ci gaba da sayar da litar man fetur a kan N145 abu ne mai wuya - Mele Kyari

Ana iya tuna cewa a watan Agustan 2015, shugaban kasa Buhari ya bayar da umarnin yin amfani da asusun bai-daya na TSA wajen biya ko kuma karbar kudade daga hannun ma'aikatu da cibiyoyin gwamnatin tarayya.

Baya ga aniyar gwamnatin Buhari na yaki da cin hanci da rashawa, tabbatar da amfanin asusun bai-daya ya bayu a sakamakon zargi da gwamnatin sa tayi na cewar gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ta wawashe asusun kasar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel