Ci gaba da sayar da litar man fetur a kan N145 abu ne mai wuya - Mele Kyari

Ci gaba da sayar da litar man fetur a kan N145 abu ne mai wuya - Mele Kyari

Mele Kyari, sabon shugaban kamfanin man fetur na kasa NNPC, ya ce abu ne mai matukar wahala a ci gaba da samar da man fetur cikin kasar nan a kan farashin naira 145 na kowace ita guda.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, sabon shugaban na NNPC ya bayyana hakan ne yayin da ya ziyarci shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, a ofishin sa na majalisar Tarayya dake babban birnin Tarayya.

A cewar sa, rahusa da farashin man fetur ke da ita a halin yanzu na da tasiri wajen angiza badakalar shigo da haramtattun kayayyaki da 'yan sumoga ke yi a kasar nan.

Yake cewa, saukin farashin naira 145 na kowace lita guda ta man fetur a kasar nan sabanin yadda ake sayar da shi a kan naira 350 cikin sauran kasashen yankin Afirka ta Yamma na taka rawar gani wajen bayar da gudunmuwar sumoga a Najeriya.

Kazalika ya ce, abu ne mai matukar wahala da babu lallai a iya ci gaba da samar da man fetur a kan naira 145.

KARANTA KUMA: Sunayen Ministoci: Buhari da shugabannin majalisar Tarayya za su gana a fadar shugaban kasa

Mele Kyari da ya ziyarci Sanata Ahmed tare da tsohon shugaban NNPC Maikantu Baru, ya ce zai ci gaba da tabbatar da kyakkyawar alaka ta hadin kai a tsakanin sa da Majalisar Tarayya domin inganta harkokin gudanarwa a bangaren da suka shafi dukkanin albarkatun man fetur da ma'adanai.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel